Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da mutum 104 da ake zargi ƴan daba ne a gaban wasu kotuna da ke unguwar Nomandsland.
An kama mutanen a wuraren hawan sallah da masarautun Kano ke yi duk shekara a bukukuwan sallah.
Wata Bakuwar Cuta Ta Yi Ajalin Mutane 45 A Kano
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Fesbuk inda ya ce ana zargin mutanen da laifukan daba da riƙe makamai da kuma ta’amali da miyagun ƙwayoyi.
Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC
Kiyawa ya ce an samu kama mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.
A baya-bayan nan ma rundunar ƴan sandan ta Kano ta kama wasu da ta ce ƴan daba ne waɗanda kuma suke addabar unguwar Ɗorayi.