Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta jingine dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, a mazabarsa.
Mai Shari’a Abdullahi Liman ya umarci shugabannin Mazabar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa, da kada su yi aiki da umarnin babbar kotun jihar na dakatar da shugaban jam’iyyar.
Umarnin Babbar Kotun Tarayyar na zuwa ne awa 24 da babbar kotun jihar ta amince da bukatar shugabannin mazabar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, saboda gwamnatin jihar mai ci na zargin sa da almundahana.
Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC
Alkalin ya hana duk wadanda umarnin kotun jihar ya shafa bin umarnin, har sai ya saurari karar da Ganduje ya shigar gabansa ne neman adalci a saurari bangarensa.
Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan nan na Afrilu domin sauraren bukatar ta shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Kano.
Hajjin Bana: Akwai yiwuwar NAHCON ta Mayar wa da Maniyata Rarar Kuɗi
Shugabannin APC na mazabar Ganduje da lauyan shugaban na APC, Jazuli Mustapha, ya shigar kara su ne Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da kuma Abubakar Daudu.
Sauran wadanda ake kara kuma su ne hukumomin tsaro da shugabanninsu.