Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda hudu tare da bayyana ma’aikatan da za su fara aiki.
Gwamna Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin Kwamishinonin ne a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya ambata cewa Mustapha Rabi’u kwankwaso a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, sai Abduljabbar Garko a matsayin kwamishinan kasa da safayo na jihar kano, yayin da aka tura Shehu Aliyu yarmedi a matsayin kwamishinan aiyuka na musamman sai Adamu Aliyu kibiya kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar.
Kotu Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje
Gwamna Yusuf ya Kuma ja hankalinsu da su zama masu gaskiya da rikon Amana a dukkannin lamuransu na yau da kullum.
Ya kuma bukace su da su maida hankali wajen bashi damar sauke nauyin da al’ummar jihar kano suka dora masa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito majalisar dokokin jihar kano tun a watan da ya gabata ne ta kammala aikin tantance sunayen sabbin Kwamishinonin da gwamnan ya tura musu domin nada su a matsayin Kwamishinoni.
Duk dai a wannan rana gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin masu bashi shawara da suma majalisar dokokin jihar kano ta sahalle masa ya nada su.