Babbar kotu a jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yiwa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wasu shugabannin APC na mazabar Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa sun ce sun dakatar da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Zargin almundahana: Ganduje da iyalansa basu halarci zaman kotun ba
Umarnin dakatarwar ya fito daga Mai sha’ira Usman Malam Na’abba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Kotun ta umarci da Ganduje kada ya kuma kiran kanshi a matsayin shugaban jam’iyyar ta APC, sannan kar ya sake shiga ko jagorantar duk wani al’amari na jam’iyyar APC.
Tinubu na son in ci gaba da zama shugaban APC – Ganduje
Dr. Ibrahim Sa’ad ne ya shigar da karar a madadin wasu daga cikin shugabannin APC na mazabar Ganduje da suka hadar da mataimakin sakatare na mazabar Lamin Sani da Halilu Gwanjo mai bada shawara kan harkokin shari’a a gaban kotun mai shari’ar Usman Malam Na’Abba.
Kotun ta umarci wadanda ake kara da cewa kowa ya tsaya a matsayinsa har zuwa ranar da za’a saurari karar a ranar 30 ga watan afirilu 2024.