Daga Halima Musa Sabaru
Allah yayiwa fitacciyar jarumar fina-finan hausa Saratu Gidado Daso rasuwa tun da asubahin wannan rana ta talata.
Ka Yi Aikin Dake Gabanka Ka Rabu Da Ganduje – Kwankwaso Ya Fadawa Abba Gida-gida
Wani Kani a wurin Jarumar mai suna Mustapha Ibrahim chigari ya shaidawa Majiyar kadaura24 cewar Marigayir a yau talata ma sai da ta dauki azumi bayan ta yi sahur ta yi sallah tace kowa dake Gidan ya je ya Kwanta ya huta sai da safe. Yace bayan goma na shafe aka ga bata tashi ba shi ne aka je domin a tashe ta ashe tuni Allah ya karbi ranta.
Rahotannin da kadaura24 ta samu sun tabbatar da cewa za,ayi, jana’izarta da karfe 4:30 na yamma.