Daga Halima Musa Sabaru
Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa shugaban limaman Harami Sheikh Abdur Rahman As Sudais ne zai jagoranci Khatamar Al-Qur’ani mai girma ta wannan Azumin na Ramadan 2024/1445.
Shehun Malamin shi ne zai jagoranci sallar tarawi ta karshe a wannan wata a masallacin Haramin makka wadda za’a gudanar a wannan rana ta lahadi .
Hajjin Bana: NAHCON ta bayyana adadin maniyyatan Najeriya da za su sauke farali a 2024
Abubunwan da ya Kamata masallata a masallacin Haramin makka su sani :
1. Karatun Khatamar Al Qur’an zai kasance tsawon mintuna 30
2. Za’a fara Addu’o’i nan take bayan an kammala karanta suratun Nas
Dan majalisar dokokin jihar kano Ibrahim kundila ya rasu
Wannan dai shi ne karo na 34 a jere duk shekara Sheikh Sudais ne ke gudanar da karatun Khatam Al-Qur’ani tare da yin addu’o’i na musamman.