Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya caccaki Ganduje

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, yace watanninsa akan karagar mulkin Kano Sun fi shekaru 8 na tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje amfani ga al’ummar jihar.

” Shekaru 8 da Kayi a Kano sun fito da gazawarka da rashin iya shugabancin al’umma, sakamakon almundahana data dabaibaye gwamnatin da kuma karkatar da kudaden al’umma da kuma rika yi, ta kowacce fuska”.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje sakamakon wata sanarwa da ya fitar inda yace gwamnan ya kasa tabukawa al’ummar jihar kano komai tun da ya Zama gwamnan jihar.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun karamar Sallah

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Lahadi.

Yace mun yi mamakin yadda Ganduje ya fito yana kalubalantar gwamnatin jihar kano, saboda yadda aka sami cin hanci da rashawa da sayar da kaddarorin gwamnatin ba bisa ka’ida ba da kuma karkatar da kudaden al’umma a gwamnatinsa.

Ya shawarci mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da su tashi tsaye wajen kare mutuncin sa a kotu, maimakon maganganun da yake yi a kafafen yada labarai.

Sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar kano ba zata bar barnar da aka yi a mulkin Ganduje ta tafi a banza ba, Inda yace dole ne su kai maganar gaban kotu domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sun Magantu Kan Labarin Rasuwarsa

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa gwamnatin jihar kano ta bukaci hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da ta bata sakamakon binciken da ta yi akan bidiyon Dala.

Sanarwar ta kara da cewa, “Muna so mu tabbatar da kudirin gwamnati mai ci da kuma shirye-shiryen mu na ganin cewa Ganduje da abokan tafiyarsa su fuskanci doka kan laifin da suka aikata da gangan.”

Gwamna Yusuf, ya ci gaba da tabbatar da cewa gwamnatinsa na da karkata ga bangarori daban-daban, tare da ba da fifiko da mai da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da na zahiri don ci gaban rayuwar Kano baki daya da kuma al’ummar jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...