Nigeria ce zata jagoranci shirin samar da matsugunni na majalisar dinkin duniya (UN-HABITAT)

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Majalisar Dinkin duniya ta zabi Nigeria a matsayin kasar da zata jagoranci shirin samar da matsugunni na majalisar dinkin duniya.

Manajan shirin na yammacin Africa Mista Mathias spaliviero ne ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci Karamin ministan Gidajen da raya birane na Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a Ofishin sa.

“Najeriya ce zata jagoranci shirin samar da matsugunni ta Majalisar Dinkin Duniya UN-Habitat,” in ji shi.

Minista Gwarzo ya bayyana jin dadinsa tare da tabbatar wa manajan shirin cewa Najeriya za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya dace domin cigaba da samun nasarar shirin.

Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano Ta Maka Ganduje, Matarsa, da Wasu Mutane 6 a Kotu

Ya nemi ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar da Shirin UN-Habitat a don tabbatar da gudirin shugaban ƙasa Bola Tinubu na Sabunta Fatan Nigeria akan Gidaje da Ci gaban Birane a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga karamin ministan Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, yace ministan ya nanata kudurin ma’aikatar wajen samar da tsaro, lafiya, da muhalli mai kyau ga daukacin ‘yan Najeriya.

Yanzu-yanzu: Kotu Ta Dakatar Da Muhuyi Magaji Rimin Gado Daga Mukaminsa

Gwarzo ya tabbatar wa da tawagar UN-Habitat cewa ma’aikatar na yin kokari wajen ganin an biya basussukan hadaka na 2022 da 2023 da suka kai dalar Amurka 500,000 cikin gaggawa.

Tun da farko Manajan shirin UN-Habitat mai kula da yammacin Afirka Mista Mathias Spaliviero ya bayyana cewa kasashe biyu na Kamaru da Kenya sun hakura sun Janye domin Najeriya ta zama shugabar shirin a wannan karon.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...