Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat Umar, Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zarge-zarge 8 da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da wasu biliyoyin nairori.
Wannan yana kunshe ne a cikin takardar tuhuma mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2024 tare da jerin shaidu 15 da aka makala.
Tinubu ya baiwa jarumar kannywood Rahama Sadau Mukami
SOLACEBASE ta ruwaito cewa wadanda ake kara a karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.
Karin bayani na nan tafe…..