Daga Kamal Yakubu Ali
Wani malamin addinin musulunci a kano khalifa sheikh Ahmad Rufa’i malam mai kasida ya bukaci al’ummar musulmi da su kara tsage damtse wajan aikata ayyukan alkhairi musamman a wadannan kwanaki goma na karshen watan Ramadana duba da irin mihimmanci da suke Dashi a wajan Allah subhanahu wata Allah.
“Waɗannan Kwanaki 10 masu albarka na karshen watan azumin Ramadan a cikin su ne Allah ya yi daren lailatul Qadri, don haka akwai bukatar al’ummar Musulmi su dage da yin aiyukan alkhairi don neman dacewa”.
Gwamnan Kaduna ya Fara Yiwa Tsohon Gwamnan Jihar El-Rufa’i Tonon Silili
Sheik Ahmad Rufa’i mai kasida ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da hudubar sallah Juma’a a masallacin juma a na muhammad Dangote dake Alfindiki a karamar hukumar Birni.
Yace Ramadan wani wata ne da ake bukatar dukkanin al’ummar musulmi su yawaita aikata ayyukan Alkhairi musamman karatun Alkurani mai girma domin Ramadan watan Alkurani ne kuma Allah yana rubanya ladan ayyuka a cikinsa.
Ramadan: Muhimman aiyuka 3 da ya Kamata mutane su rika a goman karshe – Khalifa Abdulganiyyu Getso
Yace wannan wata dama ce da Allah ya bamu domin kara neman kusanci a gareshi, domin wasu da yawa ba zasu riski wani Azimin ba, a dan haka ya kamata kowa yayi amfani da wannan dama wajan neman gafarara Allah, da Kuma yiwa kasarmu adduoin zaman lafiya da wadata musamman jahar kano da sauran jahohin musulmi baki daya.
A karshe ya yabawa mawadata dake fadin jahar nan a game da irin gudunmawar da suke bayarwa wajan rabon kayan Abinci ga ma bukata da sauran ayyukan alkhair wanda yace yin hakan zai taimaka wajan kara sanya kaunar juna da soyyaya a tsakanin alumma kamar yadda addinin musulunci ya tanadi.