Dr. Gumi ya bayyana abubunwan da suka tattauna da jami’an tsaron Nigeria

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Malamin addinin Musulunci mazaunin Kaduna, Dr. Ahmad Gumi, ya ce ya tattauna da jami’an tsaron Najeriya da suka gayyace shi kan harkokin da suka shafi tsaro .

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja cewa, jami’an tsaro sun gayyaci Dr. Gumi.

Dr. Gumi, bayan ya amsa gayyatar da jami’an tsaro suka yi masa a ranar Litinin din da ta gabata a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce shi bai fi karfin doka ba amma wadanda ba su da laifi ne kadai ke kan doka.

Yanzu-yanzu: Kotu ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukunci

Ya ce babu wani abin fargaba a gayyatar da akai masa, inda yace ya tattauna da jami’an tsaron yadda ya kamata.

“A daren jiya na samu kiraye-kiraye da yawa daga masu mutane da ‘yan jarida kan gayyatar da jami’an tsaro suka yi min da kuma tambayoyi da suka yi min.

Kungiyar DOGAA ta shirya taron shan ruwa ga daliban makarantar yan mata ta Dala

“Eh, mun sami kyakkyawar tattaunawa kan yadda za mu dakile ayyukan ta’addanci yayin da kowanne a fagensa le kokarin don magance kalubalen tsaron da ke cutar da al’umma. Mun tattauna dasu ba tare da cin mutunci sai girmamawa.

“Dukkanmu muna bukatar a matsayinmu na al’umma mu hada kai mu yi aiki tare domin samun zaman lafiya mai dorewa. Na gode da damuwar da kuka nuna a gare ni. Allah ya ci gaba da tsare mu daga dukkan sharri. Amin,”Dr. Gumi ya rubuta bayan ganawa da jami’an tsaro.

Gumi akan ta’addanci

Dr. Ahmad Gumi ya sha yin suka kan yadda jami’an tsaro ke tafiyar da ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayar da mafita ga rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.

Malam Gumi ya kuma soki yadda gwamnatin Najeriya ta wallafa sunayen mutanen da ta ke tuhuma a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci. A ranar Larabar da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana sunan daya daga cikin abokan Gumi, Tukur Mamu, tare da wasu mutane 14 a matsayin masu bada kudin ga yan ta’adda a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...