Daga Aliyu Danbala Gwarzo
An nada Sanata Abdulaziz Yar’Adua a matsayin sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.
Sanatan dake wakiltar Katsina ta tsakiya kani ne marigayi shugaban ƙasar Nigeria Umaru Yar’adua .
Nadin nasa ya biyo bayan murabus din Abdul Ningi, Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya.
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Hasken Kan Umarnin Bude Bodar Nigeria da Nijar
Majalisar dattijai ce dai ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda furucin da ya yi kan zarge-zargen a kasafin kudin 2024.
Matar Shugaba Tinubu ta bayyana dalilin da suka sa bata tsoron mutuwa
Ningi, a wata wasika da ya aike wa kungiyar, ya rubuta cewa, “Ina so in ajiye mukamina na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa. Tabbas hakan ya zama dole saboda abubuwan da ke faruwa a Majalisar Dokoki ta Kasa da Arewa da ma kasa baki daya.”
Haka kuma, kungiyar ta bayyana Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa a matsayin mai magana da yawunta da zai maye gurbin Sanata Sumaila Kawu wanda majalisar ta gargadi shi da ya daina raba mukamai da za su iya haifar da tarzoma a kasar.