Gwamnati ta ƙayyade wuraren sayar da Burodi da man fetur a Zamfara

Date:

 

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan dokar haramta sayar da biredin da ba shi da sunan kamfani da wanda ake naɗewa cikin leda da kuma sayar da fiye da lita 50 na man fetur da kuma amfani da gilashin mota mai duhu a jihar Zamfara.

Gwamna Lawal ya sa hannu kan dokar ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Gusau.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce dokar ta yi maganin matsalolin da aka bayyana suna janyo ƙalubalen tsaro a jihar.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin magance rikice-rikice a matakin farko na jihar kano

Ya ce an yi dokar ne saboda hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan wasu yankuna a sassan jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa “sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan a wasu yankuna da ke sassan wasu ƙananan hukumomin jihar musamman Zurmi da Shinkafi da Ƙaura Namoda da Talata Mafara da kuma dawowar ayyukan ƴanbindiga da sace-sacen mutane a wasu yankuna da wasu manyan tituna a jihar.

Gwamnan ya kuma haramta wa masu motoci a jihar Zamfara amfani da gilashi mai duhu sannan kuma an haramta musu rufe lambar motocinsu a lokacin tuƙi.

Matar Shugaba Tinubu ta bayyana dalilin da suka sa bata tsoron mutuwa

Abin da dokar ta ce:

Daga yanzu dole ne duk wani gidan burodi ya sanya cikakken suna da adireshi da duk wani bayani kan kamfanin.

An ƙayyade wauraren da za a sayar da burodi a fadin jihar, inda za a sayar kawai a cibiyoyin ƙananan hukumomi kawai.

A Gusau za a sayar da burodi ne a Damba-Zaria Road; Gada Biyu Sokoto Rod; Command Guest House kan hanyar Kaura Namoda; Gusau Garage-Dansadau Road.

Babu wani gidan sayar da mai wanda zai sayar da man fetur sama da lita 50 ga mota ɗaya a lokaci guda.

Gidajen sayar da man fetur za su yi aiki ne daga ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma.

An haramta rufe lambar mota a lokacin tuƙi.

Dole ne kowane mai mota ya mallaki cikakkun takardun rajista.

Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda ƴan fashin daji ke shiga ƙauyuka suna sace-sace tare da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA

Daga Usman Usman   Ambassador Maryam Hassan shugabar kungiyar wayar da...

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...