Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Manajan Daraktan Hukumar Tsar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Arc.Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin cewa hukumar sa za ta rika kai ziyara akai-akai domin tabbatar da cewa wadanda suke gudanar da gine-ginen ba bisa ka’ida ba a jiha sun bi umarnin da aka basu.
Manajan Daraktan ya bayyana haka ne a lokacin da yake duba wasu wuraren da aka gina ba tare da izini ba a jihar.
Ya nanata kudirin gwamnatin jihar na ganin an tabbatar da hana yin duk wani gine ba bisa ka’ida ba ko kuma awon igiya tare da tabbatar da bin taswirar jihar kano wajen tsara birnin Kano.
Za Mu Fara Daukar Mataki Akan Masu Yin Gine-Gine ba Tare da Neman Iziniba a Kano – KNUPDA
Arc.Ibrahim Yakub ya bayyana cewa, “KNUPDA ta fito da wani sabon salo na yadda za a iya cimma burin da aka sanya a gaba na tabbatar da jihar ta dawo kan ainahin taswirar ta don gawata birnin na kano”.
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da Jama’a ta hukumar KNUPDA Bahijja Malam Kabara ta aikowa kadaura24, tace Manajan daraktan ya bayyana cewa zasu cigaba da bibiya ba tare da kakkautawa ba don tabbatar da an dawo bin taswirar jihar kano da aka samar tuntuni.
Malam Daurawa ya bayyana sunayen wadanda suka Sulhunta su da Gwamnan Kano
A nasa jawabin mai baiwa hukumar Jawara kan harkokin shari’a, Salisu M Tahir ya bayyana cewa an kama mutane shida da suka karya dokar hukumar a yayin ziyarar, domin laifukan da suka aikata sun sabawa tanadin sashe na 12,13 da 14 na dokar KNUPDA ta shekarar 2011.
A cewarsa, an mika wadanda aka kama ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike.
Wuraren da aka ziyarta sun hada da: Tukur Road, Nassarawa GRA, Makarantar Dabo Primary, Dan Waire GGSS, Makarantar Firamare ta Mai Kwatashi, Makarantun Firamare na Na Ibrahim natsugune duk na Sabon Gari, Titin Faransa, titin Igbo, titin Warri, Sabuwar Titin, Titin Gari, Filin jirgin sama. Road, Jaba/panisau da sauran sassan Sabon Gari.