Yadda Herbert Ya Ceci Iyalaina Lokacin da Ganduje Ya Cire Ni Daga Sarkin Kano –Muhammad Sanusi II

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Alhaji Muhammadu Sanusi, tsohon Sarkin Kano, ya bayyana yadda suka rayu da tsohon Manajan darakta na Kamfanin Access holding Dr Herbert Wigwe.

Da yake magana a daren jiya asabar da aka yi bankwana domin binne Wigwe, Sanusi II ya fashe da kuka, inda ya bayyana yadda marigayin ya taimakawa iyalansa lokacin da aka cire shi daga Sarkin Kano .

Sanusi ya ce saboda ya san zai iya shiga cikin matsala , ya kewaye kansa da abokai na kirki kuma masu amana.

“Lokacin da na samu matsala a Kano, na kira shi kusan watanni shida kafin in bar Kano, na ce masa, ‘Herbert na san zaka iya yin duk mai yiwuwa bin don magance wadannan matsalolin, amma na gamsu cewa wannan abun da ya faru zai faru. Sai ya ce da ni ‘Mai martaba, kada ka damu, duk abin da zai faru, muna nan tare da kai”.

Kano: KNUPDA ta Kama Mutane 6 bisa karya dokokin hukumar

A ranar da na ji a rediyo cewa an tsige ni, da daddare kafin abin ya faru, na yi waya da shi cewa ina so in zo Legas. An sanar da hakan ne da misalin karfe tara na safe, kuma da tsakar rana Herbert ya turo jirgi Kano, inda ya dauki iyalina, ba tare da Kiran waya ko sako ba, Herbert ya karbe su, ya ajiye su a otal, kuma daga baya ya ba su masauki na tsawon watanni.”

Sanusi ya kuma ce yana tunanin zai mutu kafin Wigwe, kuma yana son ya’yansa su samu ingantaccen ilimi, hakan tasa ya damka wa Wigwe amanar kula da ‘ya’yansa.

 

“Kimanin shekaru biyu da suka gabata na fara ajiye wasu kudaden don kula karatun ’ya’yana, domin a matsayina na uba bani da abun da zan baiwa ya’yana da yafi ilimi don haka na tsara musu yadda zasu rayu ko da na mutu”.

“Na gaya wa Herbert cewa, ‘Na ba ka shugabancin wannan asusu da na samar don ilimin yarana, domin na san cewa ko da na mutu ban bar ko sisi ba, za ka ilimantar da ’ya’yana. A tunanina zan riga zan Herbert mutuwa.”

Wigwe ya mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a California, Amurka, a ranar 9 ga Fabrairu, 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...