Umarni muke Jira mu Bude Bodar Nigeria da Nijar – Kwastam

Date:

Hukamar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya, Kwastam, ta ce tana jiran ta samu umarni daga gwamnatin Najeriya, kafin ta buɗe iyakar ƙasar da makwabciyarta Nijar.

Wannan shi ne karo na farko a hukumance da hukumar ta fito ta bayyana haka, duk da kiraye-kirayen da jama’a ke ta yi kan a bude kan iyakar.

Hukumar ta ce nan ba da wani lokaci mai tsawo ba ne ta ke sa ran za a buɗe bakin iyakar.

Bidiyon Dala: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ganduje Ya Kai Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma, ECOWAS ko CEDEO ta bayyana ɗage takunkuman da ta ɗorawa Nijar, lamarin da ya kai ga rufe bakin iyakokin ƙasashen ƙungiyar da Nijar na tsawon watanni.

Malam Daurawa ya bayyana sunayen wadanda suka Sulhunta su da Gwamnan Kano

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan yulin 2023 ne Najeriya ta rufe iyakokinta da Nijar lamarin da ya haifar da ƙaruwar matsin rayuwa ga ƴan Najeriyar da kuma Nijar ɗin.

A halin yanzu akwai ɗaruruwan motocin dakon kaya ɗauke da kayan abinci da na masarufi da aka hanawa shiga Najeriyar.

Ƴan kasuwar Najeriyar sun yi maraba da umarnin cire takunkumin da ECOWAS ta yi, sai dai kawo yanzu ba su samu shigo da kayan ba saboda ci-gaba da kasancewar bakin iyakar a rufe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...