Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin karbar cin hanci da akewa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje a wani bidiyon.
Majiyar kadaura24 ta Solacebase ta ruwaito cewa alkalin kotun, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman a ranar Talata ya yanke hukuncin cewa laifin yana karkashin dokar tarayya da hukumar jihar ba ta da iko a kai.
Gwamna Abba Kabir Ya Mikawa Majalisar Kano Sunayen Kwamishinonin Da Zai Nada
Idan dai za a iya tunawa, Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya maka hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a gaban kotu inda ya bukaci alkalai da su dakatar da binciken bidiyon dala da hukumar ta ce zata yi masa.
Sai dai Lauyan wanda ake kara na farko a karar, Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Barr. Usman Umar Fari ya ce za su daukaka kara kan hukuncin kotun.
Karin Bayani na nan tafe