Hukumomi a Najeriya sun tsare wasu manyan shugabannin kamfanin Binance da ke hada-hadar kuɗi ta intanet bisa zarge-zargen “ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar”.
Babu cikakken bayani game da tsare shugabannin kamfanin na Binance sai dai rahotanni na cewa sun isa Najeriya ne domin tattauna batun dakatar da manhajar hada-hadar kuɗi tare da hukumomin Najeriya.
Gwamnan Babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa kusan dala biliyan ashirin da shida na bi ta Binance ta hanyoyi da masu amfani da manhajar da ba za mu iya tantancewa ba”.
Wa’adin Tantancewa: Kwamishinonin Kano Sun Shiga Firgici Saboda Rashin Tabbas
A hira da gidan Talabijin na Channels, Bayo Onanuga, kakakin fadar shugaban ƙasa ya zargi manhajar kirifto da sa farashin kuɗin waje a ƙasar tare da karɓar matsayin babban bankin.
“Idan ba mu fatattaki Binance ba, Binance zai durƙusar da tattalin arzikin wannan ƙasa. Kawai suna ƙayyade farashin,” kamar yadda ya bayyana.
NCC ta dauki mataki akan layukan wayoyin wasu mutane a Nigeria
Kawo yanzu dai jami’an kamfanin na Binance ba su ce komai ba kan kamen.
A disamban bara ne hukumomin Najeriya suka ɗage haramcin shekara biyu da aka ƙaƙaba kan hada-hadar kirifto saboda abin da suka kira haɗarin ɗaukan nauyin almundahana da ta’addanci daga kamfanin kirifto a ƙasar.
A 2021, gwamnati ta rufe shafin AbokiFX, fitaccen dandalin da ke bayar da bayanai game da farashin kuɗin ƙasar waje kan zarge-zargen masu dandalin na ƙayyade farashin kuɗin waje tare da janyo karyewar darajar naira a kan dalar Amurka.
Matakin baya-bayan nan da gwamnati ta ɗauka na garƙame kamfanin Binance na daga cikin matakan da take ganin zai ceci Naira da darajarta ta faɗi da kusan kashi 70 cikin 100 cikin wata takwas da ya gabata.
BBC Hausa