Daga Halima Musa Sabaru
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, a ranar Laraba, bayyana yan Nigeria tabbacin cewa ba wani ma’aikaci da zai rasa aikinsa idan an aiwatar da rahoton Oronsaye.
Muhammad Idris ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim a ranar Laraba.
Rundunar Yan sandan Kano ta Magantu Kan Batun Kamo Mawaki Ado Gwanja
Shekaru goma sha biyu bayan ta samu rahoton Stephen Oronsaye, gwamnatin tarayya a ranar Litinin, ta amince da aiwatar da wasu shawarwarin da kwamitin ya bayar na hade wasu ma’aikatu da hukumomi don rage kashe kudaden gwamnatin.
Majalisar Kano Na Shirin Wajabta Gwajin Lafiya Kafin Aure
Sakamakon haka, hukumomin gwamnati 29 za a hade su .
Bugu da kari, an mayar da hukumomi hudu zuwa ma’aikatu daban-daban guda hudu yayin da za’a soke wasu.
An gabatar da rahoton ne a cikin 2012, rahoton Oronsaye game da gyare-gyaren ma’aikatun gwamnati ya nuna cewa akwai 541 ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.
Duk da haka, Idris ya bayyana cewa, “Manufar ita ce rage kashe kudaden gwamnati da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka. Ba wai ana nufin gwamnati na shirin korar ma’aikata ko jefa mutane cikin .”
Ministan ya ce aiwatar da rahoton, ya nuna karara yadda Shugaba Tinubu ya jajirce wajen yin taka-tsan-tsan kan kasafin kudi da gudanar da mulki ta hanyar yin nazari mai zurfi a kan hukumomi, da ma’aikatun gwamnati.”