Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Hukumar tsara Birane ta Jihar Kano, KNUPDA, ta gano wasu sabbin rukunonin unguwanni 68 da aka samar da su ba bisa ka’ida ba, biyo bayan binciken da ake yi na tsaftace birnin daga gine-ginen da ake yin su ba bisa ka’ida ba.
Don tabbatar da cewa ana bin ka’idojin gine-gine a jihar kano, gwamnatin jihar ta kafa kotuna domin hukunta wadanda ke sana’ar yin gine-gine ba bisa ka’ida ba, tare da hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
Shugaban Hukumar ta KNUPDA ta jihar kano, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu, ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Ofishinsa dangane da aiyukan kwamitin da ya kafa.
Mun Dauki Matakan Hana Magudin Jarrabawa a Jami’ar Sa’adatu Rimi -Farfesa Yahya Bunkure
Ibrahim Yakubu Adamu, ya bayyana cewa daga cikin masu rukunonin unguwanni (layout) 68 din da aka gano suna ginin ba bisa ka’ida ba, masu guda 40 sun amsa gayyatar da kwamitin yayi musu, yayin da wasu suka ki girmama gayyatar da akai musu.
Ya ce, “Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ba mu cikakken ikon gudanar da ayyukan mu tare da tabbatar da cewa mun tsaftace jihar daga yawaitar gine-ginen ba tare da tsari ba, kuma duk wanda aka samu yana karya doka to tabbas za a hukunta shi.”
Rage ma’aikatu: Akwai yiwuwar ma’aikata su rasa aikinsu? Tinubu ya Magantu
Adamu ya bayyana cewa gwamnati ta sake farfado da wata doka da ake da ita a shekarar 2011, wacce ta baiwa hukumar cikakken ikon kamawa tare da hukunta duk wanda ya karya dokar tsara birane da yin gine-gine ba bisa ka’ida ba .
Sai dai kuma ya ce domin kawo karshen yin gine-gine ba bisa ka’ida ba a fadin jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da gina sabbin burane guda biyu wadanda za su kunshi dukkan wasu kayan more rayuwa da ake bukata.
Ya yi gargadin cewa ofishinsa “zai yi aiwatar da dokokin tilastawa duk wanda ya ki bin umarnin kan daina yanka filayen awon igiya da kuma yin gini ba tare izinin hukumar ba, kuma kada ku manta cewa hukuncin zaman gidan yari na watanni 3 ko watanni 6 ne akan wanda aka samu da laifin ba tare da zabin binyan tara ba”.