Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban kungiyar ECOWAS,wanda kuma shi ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bukaci kungiyar da ta sake duba tsarinta na tabbatar da amfani da kuɗin tsarin mulki a Kasashen Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar.
Da yake jawabi a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron na musamman kan harkokin zaman lafiya, siyasa da tsaro a yankin ECOWAS da ke gudana a Abuja, shugaban ya ce halin da yankin ke ciki na bukatar yanke hukunci mai tsauri .
Ya kuma bukaci kasashe uku da suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ta ECOWAS da su sake yin la’akari da matakin da suka dauka, kada su dauki kungiyar a matsayin makiyarsu.
Hanyoyi takwas da ake ku bi don sayen shinkafar kwastam mai araha
Ya ce, “Lokacin da muke ciki a halin yanzu a yankinmu na bukatar mu dauki matakai masu wahala wadanda suka sanya halin da al’ummarmu ke ciki.
“Dimokradiyya ba komai ba ce illa tsarin siyasa da kuma hanyar magance bukatu da buri na al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa dole ne mu sake nazarin tsarin da muke kai a yanzu game da neman tsarin tsarin mulki a kasashe hudu na mambobin mu. Don haka ina kira gare su da su sake duba matakin da su uku suka dauka na ficewa daga gidansu, kada su dauki kungiyarmu a matsayin makiya”.
Shugaban na Najeriya ya kuma lura da cewa, sarkakiyar batutuwan da ke tattare da su na bukatar samar da cikakken tsari da hadin gwiwa.
“Saboda haka, ya zama wajibi a gare mu mu shiga tattaunawa mai ma’ana, mu yi amfani da hankali, tare da hada kai wajen samar da mafita mai dorewa da za ta kai ga samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro tare da samar da daidaiton siyasa a yankinmu.
“Ba za a iya misalta nauyin da ke kan mu a matsayinmu na shugabanni a cikin wadannan lokuta masu wuyar gaske ba, kuma ta hanyar hadin gwiwarmu da kuma zurfin tunani ne za mu iya magance wadannan kalubale ta hanyar hangen nesa, hadin kai da kuma nauyin da ya dace,” in ji shi.