Daga Rukayya Abdullahi Maida
Falakin Shinkafi Ambassador (Dr) Yunusa Yusuf Hamza, ya shawarci gwamnatin tarayyar Nigeria da ta bada umarni ga hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Costum) rika sassautawa yan Kasuwa musamman ta fuskar biyan harajin kayan masarufi domin fitar da yan kasar daga mawuyacin halin da suke ciki.
” Babu shakka matakan da gwamnati ta fara dauka na magance matsalar hauhawar farashin Dala musamman barazanar daukar mataki akan harkar Kirifto, amma bayan wannan akwai wasu matakai da muke ganin idan an dauke su zasu taimaka wajen magance matsalar mawuyacin halin da al’umma suke ciki”.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Jaridar kadaura24 a Kano.
” Mafi yawan yan kasuwar Suna Kokawa da yadda jami’an Kwastam suke tsauwala musu ta fuskanta karbar kuɗin haraji da lissafin Dala, sannan kuma bai dace a rika yin irin tsarin ma, kamata yayi a rika amfani da kuɗin mu na Naira tunda dai so ake a saukakawa al’umma”. Inji Falakin Shinkafi
Kotun ta Yanke Hukunci Kan Kalubalantar Hukuncin Kashe Sheikh Abduljabbar
Amb. Yunusa Yusuf wanda kuma shi ne Jarman Matasan Arewa, ya ce matukar gwamnatin Najeriya tana bukatar al’umma su sami sauki dole ne sai ta sassautawa yan kasuwa ta hanyar karbar kudaden harajin kayan masarufi, wanda idan an tsauwala musu wajen kiliyarans to su ma zasu sassautawa al’umma masu siyan kayansu, haka ma idan aka tsauwala musu suma sai sun tsauwalawa al’umma masu siyan kayansu.
” Haka kuma akwai bukatar gwamnatin tarayyar tafi mai da hankali wajen karbar haraji ga kayan da basu da muhimmaci kamar sigari giya da sauran kayan kyalekyale, maimakon kayan masarufi wadanda sune al’umma suka fi bukatarsu a yau da kullum”. A cewar Falakin Shinkafi
Majalisar dokokin jihar Kano ta bankado badakalar kudi a wasu hukumomin gwamnati
Game da batun cire tallafin wutar lantarki da gwamnati ta ce zata yi, Amb. Yunusa Yusuf Hamza yace bai kamata gwamnatin ta cire tallafin ba a irin wannan lokaci da al’umma suke cikin radadin cire tallafin man fetur.
” Ko shakka babu idan aka cire tallafin wutar al’umma zasu kara shiga cikin mawuyacin hali, don haka muna shawartar shugaban kasa da duk masu ruwa da tsaki a harkar da su tabbatar ba’a cire tallafin wutar lantarki a Nigeria ba”. Inji Falakin Shinkafi
Yace waɗannan abubunwan da ya fada idan gwamnatin tarayyar Nigeria ta karbe su kuma ta aiwatar da su, babu shakka al’ummar kasar zasu sami saukin na mawuyacin halin tsadar rayuwar da suke ciki a yanzu.