Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar kula da gidan gyara hali ta kasa reshen jihar kano ta bayyana cewa tun ranar Alhamis ta saki Murja bisa umarnin kotu.
Tun a daren jiya dai ake ta rade-radin an nemi Jarumar TikTok din Murja Ibrahim kunya a gidan gyaran hali an rasa ta, wanda hakan tasa Ake zantuka da korafe-korafe akai musamman a dandalin sada zumunta.
Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa Daily Nigerian hakan a yau lahadi.
Kano: NAFDAC da Gargaɗi Kamfanoni Game da Yan Kasuwar Magani na Sabon Gari
“Sananniyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya ba guduwa ta yi daga gidan yari ba mu ne muka sake ta bisa Umarnin kotu” inji Musbahu Kofar Nasarawa
A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta tun a ranar.
Kotu a Kano ta Aike da Murja Kunya Gidan Yari
Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito hukumar Hisbah ta jihar kano ce ta gurfanar da Murja Ibrahim kunya bisa zarginta da yin aikata bidala da kuma kokarin ta da hankali al’ummar unguwar Tinshama inda acan ne murjar take zaune.