Ma’aikacin Radio Nigeria, ya zama shugaban kungiyar tsofaffin daliban Federal Polytechnic K/Namoda

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda dake jihar Zamfara, a babban taronta na farko cikin shekaru 41 da kafuwarta, ta zabi Abdulrazak Bello Kaura, sakataren kungiyar ‘yan jarida ta shiyyar Arewa maso Yamma, a matsayin shugaban kungiyar tsofaffin daliban na kasa baki daya .

Abdulrazak Kaura, sakataren NUJ na Arewa maso Yamma, ya samu kuri’u 124 a zaben da aka gudanar a makarantar, inda ya doke abokiyar hamayyarsa, Viashima Leonard, wadda ta samu kuri’u 112. Mista Audu Yahwa, Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na kungiyar ne ya sanar da hakan.

“Abdulrazak Bello, da ya samu kuri’u mafi rinjaye kuma ya cika sharuddan, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma a zabe da aka gudanar,” in ji Audu Yahwa.

Maryam ta Fim din Labarana ta bayyana kalubalen da ta fuskanta bayan fitar Shirin

Sauran ’yan takarar da suka lashe zaɓen ba tare da habayya ba sun hada da Hassan Bamidele (Mataimakin Shugaban kungiyar na kasa), Rimamyang Amos (Sakatata), Ezekiel Luka (Mataimakin Sakatare), Kabiru Ibrahim (Sakataren Kudi), Abdulsabur Hassan (Ma’aji), Idris Garba (Jami’in Jin Dadi), da Olufemi Ebenezer a matsayin Sakataren Yada Labarai.

An kafa makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda a shekarar 1982 kuma yanzu haka tana da dalibai sama da dubu hamsin da suka yaye a fannoni daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam...