Iftila’i: Goodluck Jonathan ya Mika Kokon Bararsa ga Yan Nigeria

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

Tsohon shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa mahaifiyarsa, Mama Eunice Afeni-Jonathan addu’a da iyalansa bayan rasuwar yayarsa Madam Obebhatein.

Jonathan ya ce mutuwar Madam Obebhatein ta daga hankalin mahaifiyarsu.

Ya bayyana hakan ne a yayin jana’izar Madam Obebhatein a Otuoke, karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa ranar Juma’a.

Kotu a Kano ta Aike da Ramla Yar TikTok Gidan Yari

Jonathan ya bayyana cewa Madam Obebhatein, wacce ta mutu tana da shekaru 70 a ranar 11 ga Janairu, 2024, ita ce ‘ya mace tilo da ta rage wa mahaifiyarsa.

A cewarsa: “Mutuwa, kamar yadda suka ce, tana kan kowa. Amma lokacin da mutum zai mutu shi ne abun ji. Eh, duk za mu mutu wata rana amma lokaci ba wanda yasan lokacin.

“Yar’uwata ta mutu a lokacin da mahaifiyar mu take bukatar ta, don haka nake ganin zata iya shiga wani yanayi bayan mutuwarta ta, don haka nake bukatar kusa ta a addu’o’in ku” .

Bincike: Dalilan da Suka sa Farashin Kayan Abinchi ya fara Karyewa a Kano

“Dole ne in yi godiya ga uwargidan gwamnan jihar Bayelsa da sauran matan da suka zo kusa da ita domin lokacin da yayar tawa ta mutu ina Landan”.

“Da kun san yadda ta kasance da kuma yadda take a yanzu, da kun san cewa har yanzu tana cikin damuwa. Don haka kucigaba da yiwa mahaifiyata addu’a. Allah yasa mu dace. Na gode.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...

Ni da kaina na je ofishin EFCC – Ajiya

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na...