Bincike: Dalilan da Suka sa Farashin Kayan Abinchi ya fara Karyewa a Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Rahotanni na nuni da cewa kayan abinchi sun fara saukowa a jihar kano dake Arewacin Nigeria, sabanin yadda aka saye su a makon da ya gabata.

Binciken da jaridar kadaura24 ta gudanar ya nuna cewa saukar farashin kayan abinchin yana da nasa da matakin da Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano ta gudanar.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar lahadin da ta gabata shugaban hukumar karbar korafe-korafen da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado ya kai samame kasuwar dawanau musamman Wuraren ajiyar kayan, inda ya kama Wuraren ajiyar kayan abinchi makare da kayan masarufi kamar Taliya da Sukari da dai sauransu.

Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago zata gudanar da zanga-zanga a fadin Nigeria

Bayan kama kayan ne shugabannin kungiyar Singa suka ziyarci Muhuyin tare da yi masa alkawarin zasu rage farashin kayan masarufi kafin zuwan azumin watan Ramadana.

Hakan ce tasa a wannan makon musamman daga ranar larabar da ta gabata al’umma suka fara samun saukin kayan abinchi.

Jaridar kadaura24 ta shiga cikin kasuwar yan hatsi ta dawanau a jihar kano Nigeria domin Jin yadda farashin kayan suke a kasuwar , Inda muka iske kayan abinchin musamman dangin hatsi suka fara saukowa.

Rashin isassun yan sanda ne yake dakile yunkurin mu magance matsalar tsaro a Nigeria -Babban Sufeton

Ga yadda farashin buhun kayan yake a makon da ya gabata da kuma yadda ake sayar dasu a yau:

1. Masara 57,000 yanzu kuma 47,000 zuwa 48,000

2. Dawa 50,000 yanzu kuma 44,000 zuwa 45,000

3. Gero 57,000 yanzu kuma 50,000 zuwa 51,000

4. Shinkafa Shan shara 44,000 yanzu kuma 33,000 zuwa 33,500

Rahotanni da muka hada sun tabbatar da cewa matakin da Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano ta dauka ya taimaka matuka wajen fito da kayan da kuma karyewar farashin.

Ko a jiya yayin wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu yayi da gwamnonin Nigeria ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa wancan aikin da ta yi na fara kama masu boye kayan masarufin tare kuma da umartar sauran jihohi da su yi koyi da Kano.

Haka zalika, Shugaba Tinubu ya baiwa hukumomin tsaro Umarnin kama duk wanda aka samu da boye kaya a duk fadin Kasar. Umarnin da Za’a iya cewa ya fara aikin domin a safiyar yau juma’a kadaura24 ta rawaito cewa hukumar kare hakkin mai saya da mai sayarwa ta kasa a tufe Kantin Sahad stores dake Babban birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...