Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago zata gudanar da zanga-zanga a fadin Nigeria

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar kwadago kafin cikar wa’adin kwanaki 14 don kaucewa zanga-zanga a fadin kasar.

Kwamared Joe Ajaero ya bayyana haka ne bayan taron majalisar zartarwar kungiyar ta kasa ranar Juma’a a Abuja.

Kwamared Joe Ajearo ya ce NEC ta amince da fara zanga-zangar matukar ba a biya bukatun kungiyar kwadagon ba.

Da dumi-dumi: Hukumar Hisbah ta sake kama wata yar TIKTOK a Kano

Shugaban kungiyar Kwadagon ya jaddada cewa zasu gudanar da zanga-zanga a duk fadin Nigeria a ranakun 27 da 28 ga wannan wata sakamakon tsadar rayuwa da yan Nigeria suke fuskanta.

Matsalar tsaro: Malam Shekarau ya baiwa Tinubu Shawara

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Dr Nkieruka Onyejeocha ya tabbatar wa kungiyar kwadagon cewa gwamnatin tarayya za ta cika yarjejeniyar da aka cimma da Organised Labour.

Akalla an kulla yarjejeniya kusan guda 16 tsakanin gwamnatin tarayya da Kungiyar Kwadago ta NLC da TUC tun a watannin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...