Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta tabbatar da Kama wasu mutane uku da take zargi da hallaka wani yaro dan kimanin Shekaru 14 a duniya, da suka yi Garkuwa da shi a unguwar mariri dake Jihar.
A ranar 08/02/2024 da misalin karfe 1100 na safe ne aka samu rahoto daga wani Alhaji Rabiu Abdullahi mazaunin unguwar Hotoron Fulani, cewa wani da ba’a sani ba ya bugo masa waya cewa dansa Abdullahi Sani mai shekaru 14 a duniya, sun yi garkuwa da shi, kuma suna bukatar nemi kudin fansa Naira Miliyan Hudu (N4,000,000:00) domin a sake shi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Da dumi-dumi: Kotun Shari’ar Musulunci ta Kwace Kaddarorin Sha’aban Saboda Bashi
Sanarwar tace kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Usaini Gumel, yace jami’ansu sun kama babban wanda ake zargin Ismail Adamu, mai shekaru 22, mazaunin unguwar Hotoron Fulani Kano a ranar 12/02/2024.
“A ci gaba da binciken, Ismail Adamu ya amsa laifin hada baki da wani Risi, dake zaune a unguwar Mariri tare da yin garkuwa da wanda aka kashe. Wanda ake zargin ya ce sun kai wanda aka kashen zuwa kauyen Sabuwar Zara inda suka daba masa wuka a wuyan sa suka jefa shi a cikin rijiyar bahaya ( Soakaway) a wani gini da ba a kammala ba, inda daga bisani suka tuntubi mahaifin suka bukaci Naira miliyan hudu (N4,000,000). :00) domin a sake shi”. A cewar sanarwar
Aminu Dantata ya Bayyana Ra’ayinsa Kan Batun Sauya Tsarin Shugabanci a Nigeria
Sanarwar tace ” jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru inda aka dauke gawar marigayin daga Soakaway aka kaita Asibitin kwararru na Abdullahi Wase dake Kano inda wani Likita ya tabbatar da mutuwar shi kuma aka ajiye gawar a dakin ajiye gawa na Asibitin.
” Binciken da aka yi ya kai ga kama wasu mutane biyu; wato Musa Usman mai shekaru 17, da Abdullahi Usman, mai shekaru duk mazaunan unguwar Hotoron Fulani, Inda sanarwar ta ce Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yabawa al’ummar jihar kano bisa goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar, inda ya jaddada cewa zasu cigaba da aiki tukuru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.