Sarkin Musulmi ya bayyana dalilansa na cewa Najeriya tana kan tsini

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayyana fargabar cewa Najeriya na fuskantar barazanar tsaro bisa la’akari da yadda dumbin matasan kasar ke fama da rashin aikin yi da yunwa.

Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jawabi a wani taron majalisar sarakunan gargajiya ta arewacin Najeriya ranar Laraba a Kaduna.

Muhammad Sa’ad Abubaakr III ya ce ” mun shiga wani sabon zango na shugabanci. An samu sabbin gwamnoni inda kuma wasu suka yi tazarce a karo na biyu amma har yanzu muna fama da matsalar tsaro.

Yadda Yan Majalisa ke Kokarin Mayar da Nigeria Tsarin Firaminista

Babban matsalar ma ita ce karuwar talauci. Mafi yawancin mutanenmu ba su da hanyoyin samun abin da za su ci su sha”.

Ya kara da cewa idan dai har gwamnoni na son zaman lafiya a jihohinsu, dole ne su sama wa matasa aikin yi sannan dole ne su yi aiki tare da sarakunan gargajiya.

Yadda Zaman Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ya Kasance Kan Batun Yajin Aiki

“Dole ne mu sama wa dimbin matasanmu masu zaman kashe wando ayyukan yi. Na sha fadar cewa muna wasa da bakin wuta. Saboda samun miliyoyin matasa ba tare da ayyukan yi ba sannan suna fama da yunwa, hakan na nufin muna fuskantar barazana.”

Daga karshe ya ce ya yi amannar cewa za a samu mafita duk da cewa “Najeriya ba ta taba gaza samar da mafita ba illa dai kawai ba a iya aiwatarwa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...