Noma/Ruwan Famfo: Al’ummar Bagwai na Yawaba Gwamnatin Kano – Iliyasu Wakili

Date:

Daga Shu’aibu Sani Bagwai

 

Tsohon Shugaban Kwamitin samar da ruwan sha na matatar ruwa ta Watari da ke Bagwai, Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya yaba wa kokarin gwamnatin Jihar Kano na samar da ruwan famfo ba tare da katsewa ba a yankin Bagwai da kewaye.

Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a yankin.

Ya ce babu shakka gwamnatin Jihar Kano ta cancanci yabo a wannan bangare musamman yadda al’umar Bagwai da kewaye ke samun wadataccen ruwan famfo a koda yaushe duk da wannan yanayi da ake ciki na tsadar man Gas.

Gwamnan Kano ya bada wa’adi da sharadi domin sauke wasu kwamishinoni

Haka zalika tsohon Shugaban Kwamitin ruwan ya yi maraba da wani yunkurin gwamnatin Jihar tare da hadin gwiwar bankin bunkasa harkokin musulunci na duniya na fara aiwatar da aikin fadada wuraren noman rani da ke Bagwai da kewaye wanda ya kai hekta dubu daya.

Ya ce wuraren da wannan aikin ya shafa sun hada da Bagwai da Dogon Dawa da Dullu da kuma Kauyen Adam a matsayin wuraren aikin noman rani na sashi na daya zuwa na 6.

Yadda Zaman Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ya Kasance Kan Batun Yajin Aiki

Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya Kara da cewa babu shakka idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma karuwar arziki a tsakanin al’umar yankin da ma Jihar Kano baki daya.

Alh Iliyasu Wakili Bagwai wanda kuma tsohon ma’aikacin ma’aikatar noma ne, ya bukaci al’umar wannan yanki na Bagwai su yi amfani da wannan damar wajen dogaro da kansu ta hanyar kama sana’ar noma gadan-gadan musamman noman zamani da kuma baiwa gwamnati hadin kai a manufofinta domin inganta rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...