Yadda Zaman Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ya Kasance Kan Batun Yajin Aiki

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin N35,000 da ta fara biyan ma’aikata domin rage radadin illar cire tallafin man fetur ga ma’aikatan ƙasar.

Gwamnatin ta kuma roki kungiyar kwadagon kasar da su janye yajin aikin da suka shirya yi na kwanaki 14.

Gwamnan Kano ya bada wa’adi da sharadi domin sauke wasu kwamishinoni

Karamar ministar Kwadago ta Najeriya, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bada wannan tabbacin a Abuja a wajen wani taro da shugabannin ƙungiyoyin kwadagon biyu da aka yi kan wa’adin da suka bai wa gwamnati na tafiya yajin aiki idan ba ta cika musu bukatunsu ba a cikin makonni biyu.

An dai cimma yarjejeniyar ne ranar 2 ga Oktoba, 2023 mai dauke da abubuwa 16 da suka hada da ƙarancin albashin ma’aikata da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata duk wata da dai sauransu.

Kotu a Kano ta Aike da Murja Kunya Gidan Yari

Onyejeocha ta kuma ce gwamnati ta kara kaimi wajen ganin an kammala aiwatar da wannan yarjejeniya.

Ministar ta kira taron ne domin bayyana wa ƙungiyoyin kwadagon yadda ake aiwatar da yarjejeniyar, da kuma jaddada aniyar gwamnati kan yarjejeniyar.

“Gaskiya ne da cewa mun kulla yarjejeniya, amma gwamnati ta nuna gaskiya kan wannan batu, kuma bisa la’akari da gaggawar lamarin ne na kira wannan taro domin tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa a kodayaushe, kuma dukkan mu muna neman lafiya kasancewar mutanenmu.”

Ta yi nuni da cewa, yayin da martanin kungiyoyin kwadagon kan gazawar gwamnati na cika yarjejeniyar bai dace ba, yana da kyau ayi la’akari da cewa wasu abubuwa da ke cikin yarjejeniyar ba za a iya cim musu ba a lokaci guda.

Rahotanni sun ce an tashi daga taron ba tare da cimma wata matsaya ba dangane da bukatun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...