Gwamnan Kano ya bada wa’adi da sharadi domin sauke wasu kwamishinoni

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir, a ranar Talata ya gabatar da kudirin sauke kwamishinonin da ba su yi aiki ba a majalisarsa.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun lokacin da gwamnan ya rantsar da kwamishinonin ta watan Yuni, 2023, ya umarci kwamishinonin da su mayar da hankali wajen aikin su idan kuma ba haka zai tsige duk wanda aka samu Bai tabuka komai ba.

Kotu a Kano ta Aike da Murja Kunya Gidan Yari

Don haka gwamnan ya umurci sakataren gwamnatin jiha (SSG) da ya bayar da fom tantancewa ga kwamishinonin domin su cike, kuma da shi ne za’a yi amfani wajen gano kokarinsu ko akasin hakan .

Gwamnatin Tarayya Tace ta Gano Hanyoyin Magance Hauhawar Farashin Abinchi a Nigeria

Gwamnan ya baiyan hakan ne yayin taron Majalisar zartarwa ta jihar taro 12, Wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace zai dauki matakin tsige duk wanda aka samu bai tabuka komai a Ofishinsa ba, tare kuma da maye gurbinsa da wani.

Gwamnan yace ana bukatar kowanne kwamishina ya mayar da fom din da aka bashi nan da Kwanaki 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...