Gwamnan Katsina Ya Bayyana Yadda Yan Bindiga ke Farautar Ran sa

Date:

Daga Hafsat Yusuf Abubakar

 

Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya bayyana cewar ’yan bindigar da jami’an tsaro suka hana sakat a jihar na ci gaba da farautarsa domin kawo masa hari, sai dai hakan ba zai sa ya ɗaga kafa a kokarin sa na kakkabe su daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya ba.

Gwamnan ya ce bayanan sirri kan harkokin tsaro sun tabbatar da haka, amma ko da sunan wasa babu abin da zai razana shi wajen ganin ya kauda kai daga alkawarin da ya yi wa Katsinawa na samar musu zaman lafiya.

Radda ya bayyana cewar nasarar da ake samu a kan ’yan ta’addan shi ne ke musu zafi, saboda haka jami’an tsaro za su ci gaba da aikin su wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

Tsadar Rayuwa: Abubuwan da Ɗangote yayi alkawarin taimakawa al’ummar Kano da su

“Rahoton tsaro ya nuna cewa a yanzu ina ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙoƙarin kaiwa hari a jihar saboda matakan da muke ɗauka na shawo kan lamarin.”

Gwamnan ya kuma bayyana matukar damuwa a kan yadda ake safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen makota, abin da ke haifar da tsadar su yanzu haka.

“Abin takaici ne yadda farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi ke karuwa a kullum, don haka akwai buƙatar masu ruwa da tsaki su ba da shawarwari masu amfani a kan matsalar.

Tinubu Ya Bayar da Sabon Umarni ga Yan Nigeria

“An sanar da ni cewa ana jigilar kayan abinci daga kasuwanninmu zuwa kasashe makwabta kamar Nijar, har zuwa Mali da Burkina Faso, saboda darajar Nairar mu ta tabarbare yayin da nasu kuɗaɗen ke kara daraja.

Irin waɗannan mutane suna amfani da wannan damar wajen cutar da talakawa. Wannan babbar matsala ce da ba za mu iya nade hannayenmu mu kyale ta ci gaba ba.”

Ya bayyana hakan ne yayin gudanar da wani taron gaggawa na majalisar tsaro wanda aka gayyaci sauran jiga jigan jihar domin tattauna wasu daga cikin matsalolin da suka addabe ta, ciki har da da matsalar tsaro da kuma tsadar kayan masarufi.

A taron wanda aka gudanar a ranar Juma’a, Radda ya yi alkawarin kafa kwamitin da zai aiwatar da yarjejeniyar da taron manyan mutanen jihar ya cimma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...