Daga Aisha Aliyu Umar
Gamayyar kungiyoyin masu makarantu masu zaman kansu a jahar kano sun bayyana janye karar da suka shigar da gwamantin jihar kan ayyukan hukumar makarantu masu zaman kansu .
shugaban gamayyyar kungiyoyin masu makarantun a jihar kano Injiyana Bashir Adamu Aliyu ne ya tabbatar da hakan jin kadan bayan kamala sanya hannu a takaddun yarjejeniyar fahintar juna tsakanin hukumar lura da kuma masu makarutu masu zaman kansu bisa kulawar ma’aikatar shari a ta jahar kano.
Da dumi-dumi: Kungiyar Kwadago ta Bayyana Ranar Fara Yajin Aiki a Nigeria
” Mun zauna da wakilan gwamnatin kusan Kwanaki 10 da suka gabata, kuma mun cimma matsaya hakan tasa muka Sanya hannu kan yarjejeniyar a wajen kotun don haka zamu janye karar da muka kai gwamnatin jihar Kano “. Inji Adamu Aliyu
Yace a matsayin su na shugabannin kungiyoyin makarantu masu zaman kansu zasu cigaba da bin ka’idojin gwamnati domin samar da ingantaccen ilimi ga al’ummar jihar kano.
Da yake jawabi Kwamishinan sharia na jihar kano Barista Haruna Isah Dederi wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Mustafa Muhammad ya bayyana yadda zaman sulhun ya kasance tare da kiran bangarorin biyu su rinka tattaunawa lokaci zuwa lokaci don Karin fahintar juna.
” Gwamnatin jihar kano bata da nufin muzgunawa masu makarantu masu zaman kansu, muna kokarine kawai don su kyautata aikin don samar da ingantaccen ilimi ga yaran a jihar kano”. A cewar Mustafa Muhammad
Yace sun sami fahimtar juna tsakanin su da Kungiyoyin, yanzu sun dinki duk wata matsala dake tsakanin, kuma nan bada jimawa zasu sanar da kotu cewa sun warware rikicin dake tsakanin su.
Tun da farko da yake jawabi mai bawa Gwamnan kano shawara kan makarantu masu zaman su a kano Comrade Baba Abubakar Umar yace hukumar bata da nufin tsaurarawa masu makarantun saidai kawai domin tabbatar da cewa ana bin doka da Gwamnatin jahar Kano samar.
Taron zaman sulhun dai ya gudana a maaikatar shariar ta jahar kano.