Jinkirin biyan albashi: Ma’aikatan gwamnati sun kalubalanci Tinubu

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Wasu ma’aikatan gwamnati sun zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da rashin kula da halin da ma’aikata ke ciki.

Ma’aikatan ta hanyar kungiyoyinsu sun yi wannan zargin ne kan jinkirin da ake samu na biyan albashi, tagomashi da sauran kudaden alawus-alawus.

Tsadar Kayan Abinchi: Kotu Ta Baiwa Gwamnatin tarayya Umarni

Kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta ƙasa, ASCSN, ta bayyana rashin jin dadin ta musamman kan jinkirin biyan albashin ma’aikata na wata-wata.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, Tommy-Etim Okon, Shugaban ASCSN ya ce ya kamata gwamnati ta gaggauta biyan albashi da alawus din ma’aikata.

Gobara ta Kone Kayan Abinchi da Dabbobi a Kano

Ya ce, tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki, ba a biyan albashin ma’aikata a kowane wata a kan lokaci, wanda hakan ke shafar samar da ayyukan yi da walwala.

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta kula da halin da ma’aikata ke ciki, duba da irin halin kuncin da ake ciki a kasar nan.

“Kowace rana tsadar rayuwa tana kara hauhawa, ta yaya ma’aikata za su biya kudin mota zuwa ofis, ta yaya tattalin arziki da sauran masana’antu za su tsira, idan ba a samun hada-hadar kudade?

“Yau ne 8 ga Fabrairu, kuma zan iya gaya muku sarai cewa har yanzu ma’aikata da yawa ba su karbi albashinsu na watan janairu ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...