Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta Bayyana Yadda Zata Yaki Yan Kasuwa Masu Boye Kayan Masarufi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta sha alwashin kwace kayan da aka boye tare da gurfanar da masu su a gaban Kotu sakamakon tashin farashin kayayyaki.

Barista Muhyi Magaji, Shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Kano dangane da hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa hukumar za ta dauki kwakkwaran mataki a kan mutanen da aka samu suna boye kayan masarufi a jihar Kano.

Jinkirin biyan albashi: Ma’aikatan gwamnati sun kalubalanci Tinubu

Ya kamata wadanda ke yin tara kayan masarufi su daina,” in ji Barista Muhyi Magaji.

“Hukumar mu ba za ta zuba idanu ba ’yan kasuwa su rika boye kayayyaki masarufi ba. Mu mun san akwai maganar tashin farashin dala, amma wadanda suke boye kaya, ko da ma’aikatar kasuwanci ta tarayya ba ta dauki mataki ba, mu za mu kwace kayan da aka boye, mu kuma gurfanar da mai shi a gaban kotu.” a cewar Muhuyi

Gobara ta Kone Kayan Abinchi da Dabbobi a Kano

Da yake nuna damuwa kan yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki, Barista Muhyi Magaji ya jaddada aniyar hukumar na cika aikin ta. “ wannan shi ne muhimmin bangare na aikinmu,” in ji shi, yana mai jaddada girman lamarin.

Da yake karin haske kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka, Barista Muhyi Magaji ya bayyana kokarin da ake yi na tunkarar kalubalen “Mun ziyarci kamfanonin shinkafa inda suka ce suna bada sarin shinkafar akan kuɗi Naira dubu 58 ,” in ji shi.

Duk da haka, ya kuma yarda cewa baya ga tashin farashin dala da manufofin gwamnatin tarayya na sauya fasalin tattalin arzikin kasa, suma yan Kasuwa suna tsauwalawa mutane wanda hakan ya kara ta’azzara lamarin.

Yayin da hukumar ke shirin daukar tsauraran matakai na hana boye kayan masarufi, masu ruwa da tsaki na sa ran za a sake mayar da hankali wajen ganin yan Kasuwa sun daina tsauwalawa mutane.

Yunkurin kwace kayayyakin da aka boye tare da daukar matakin shari’a kan masu laifin na kara jaddada aniyar gwamnati na kiyaye muradun al’umma .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...