Daga Kamal Yakubu Ali
Wani malamin addinin musulunci anan kano sheik Barrister Habib muhammad dan almajir fagge, yace dole sai matasa sun tsage damtse wajan neman ilimin addinin musulunci da kuma karatun sana’a, wanda zai basu damar dogaro da kawunansu Wanda hakan zai taimaka masu wajan kasancewa mutane na gari.
” Matasa sune kashin bayan cigaban al’umma don haka ya zama wajibi idan ana bukatar samun al’umma ta gari kowanne matashi ya zamana yana da Sana’ar yi da kuma ilimin addini”.
Jinkirin biyan albashi: Ma’aikatan gwamnati sun kalubalanci Tinubu
Sheikh Dan almajir ya bayyana hakane a bikin saukar karatun Littafin muwada na imamu malik da ya kwashe shekaru goma sha uku ana yana koyarwa a farafajiyar makarantar dake masalallacin juma’a na Daiba dake unguwar
Rinjyar lemo.
A yayin taron sheikh imam Barrister Habib dan almajir ya bayyana farin cikinsa game da yadda daliban suke bada goyan baya wajan halartar karatuttukan da ake gabatarwa ba tare da nuna gazawa ba.
Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta Bayyana Yadda Zata Yaki Yan Kasuwa Masu Boye Kayan Masarufi
Yace baiwa dalibai ingantaccen ilimi da tarbiyya shi ne babban jigo na samun nasara a cikin rayuwarsu a duniya da lahira.
Taron ya samu halartar al’umma da dama wadanda suka hadarda khalifa Ahmad muhammad Dan almajir Alhaji Ali Abdurrahman da Alhaji Aminu sadauki