Da dumi-dumi: An kai Batun Rushe Masarautun Kano da Mayar da Sanusi Matsayin Sarkin Kano Gaban Majalisa

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rusa dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta shude ta kafa, sannan sun nemi a maido da tsohon Sarkin Kano Sanusi II.

Wata kungiyar a wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024 da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, ta ce rusa masarautu tare da maido da Sanusi a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano”.

Tsadar Kayan Abinchi: Tinubu na Ganawa da Masu Ruwa da Tsaki

Wasikar tana cewa:

“Mun rubuto wasikar ne don rokon a wannan majalisa data yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu.

“Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za a fi samun hadin kai da cigaban al’ummar Kano. Rushe masarautun zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman Wannan gida zai yi abun daya dace daidai da doka.

Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano, A Karon Farko

Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan harkokin tafiyar da masarautu.

“Duk da haka, cikin kaskantar da kai muna rokon majalissa da ta sake duba matakin tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano .”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...