Ƙaranci Sadaki: Mal Ibrahim Khalil ya kalubalanci Batun Naira 100, ya fadi hakikaninsa

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shugaban majalisar malamai ta jihar kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa ba’ayi amfani da ilimin addini ba, waje cewa yanzu mafi ƙaranci sadaki ya haura Naira dubu chasa’in .

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata wasu kafofin yada labarai sun rawaito cewa fadar Sarkin musulmi ta fitar da cewa mafi ƙaranci sadaki yanzu a Nigeria ya haura Naira dubu chasa’in.

Da dumi-dumi: An kai Batun Rushe Masarautun Kano da Mayar da Sanusi Matsayin Sarkin Kano Gaban Majalisa

” Bai kamata a yi amfani da yadda ake chanji Dala ko tsadar kayan da ake fama da su a yanzu ba, saboda kirkirarru ne , shi kuma Addinin Musulunci kullum sauki yake kawo wa mutane ba azabtar da su ba, don haka akwai kuskure a ce mafi ƙaranci sadaki ya haura Naira dubu chasa’in”.

Kadaura24 ta rawaito Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan be yayin wata karatu da aka saba sakawa a sahihin shafinsa na Facebook.

Yunwa: Rarara ya raba kyautar kayan Abinchi da kuɗin cefane ga magidanta

” Magana ta Gaskiya wadda ta dace da hankali ita ce mafi ƙaranci sadaki yana nan a Naira dubu 20 , Amma idan mutum yana da hali zai iya karawa zuwa abun da ya sawwaka , don haka ku yi watsi da batu Naira dubu chasa’in a matsayin mafi ƙaranci sadaki”.

Malam Ibrahim Khalil ya yi suka Mai zafi cikin mushin kan yadda aka fitar da wancan bayani na mafi ƙaranci sadaki, inda yace idan aka biyewa wancan batun to da yawa ba zasu iya yin aure ba, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin al’umma suke ciki a yanzu.

Ya tabbatar da cewa mafi ƙaranci sadaki naira 20 ne kuma ya kafa hujjoji da ayoyi da hadesan Annabi Sallahu alaihi wasallam da kuma fatawoyin malamai masu tarin yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...