Daga Hafsat Yusuf Abubakar
Shahararren mawakin Siyasar Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya Tallafawa Mutane Dubu Goma ( 10,000 ) da Kyautar Kayan Abinchi, domin rage musu radadin halin tsadar rayuwar da Ake fama da ita.
Sannan Kuma ya baiwa kowanne daga cikinsu na dubu 5 kuɗin cefane, inda yace ya kashe kimanin Naira Miliyan Hamsin (50,000.000 ).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadin min Rarara kan harkokin yada labarai Rabi’u Garba Gaya ya aikowa kadaura24.
Iftila’i: Gobara ta Hallaka Wani Yaro Dan Shekara 4 a Kano
Yace ya bada tallafin ne domin rage wa al’ummar garinsu na kahutu dake karamar hukumar Danja a jihar Katsina wahalar da suke ciki.
Mun Dukufa Neman Hanyoyin Magance Tsadar Kayan Abinchi a Nigeria – Tinubu
Dama dai an jima ana kira ga wadanda suke da hali da su tallafawa al’umma musamman makotansu ko na kusa da su don rage musu radadin halin tsadar rayuwar da ake fuskanta a Nigeria.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka gudanar da rabon: