Yanzu-yanzu: Shugaban Karamar hukumar Nasarawa ya koma NNPP Kwankwasiyya

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Shugaban Karamar hukumar Nasarawa Auwal Lawan Shu’aibu wanda aka fi sani da aranposu ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP mai mulkin jihar Kano.

“Ungulu ta Koma gidanta na Tsamiya…….. Kuma fa His Excellency “ABBA KABIR” Masoyin talakawa ne da Kano, mucigaba da tayashi da adu’a” . A cewar Aranposu

Da dumi-dumi: Shugaban Karamar Hukuma a Kano Ya Ajiye Aikinsa

Auwal Lawan ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a safiyar talatar nan.

Tun da sanyin safiyar wannan rane dai aka wayi gari da wasu hutunan shugaban karamar hukumar ta Nasarawa da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf yayin wata ziyara da ya kai masa.

Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano, A Karon Farko

A hotunan an ga Aranposu sanye da jar hula Wanda hakan Ke nuni da cewa ya koma tafiyar Kwankwasiyya da ya bari tun lokacin da aka raba gari tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Dama dai Aranposu yayi kaurin suna wajen sukar dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC duk da sun fito a karamar hukuma guda.

Kwanaki kadan ne dai suka ragewa shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...