A halin yanzu dai kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa a sha’anin Abinchi na gudanar da taro a fadar shugaban kasa dake Abuja kan tsadar rayuwa a Nigeria.
Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikata fadar shugaban kasa ne ya kira kwamitin din, wanda shugaban kasa Bola Tinubu zai jagoranci.
Yunwa: Rarara ya raba kyautar kayan Abinchi da kuɗin cefane ga magidanta
Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA); Yemi Cardoso, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN); Tahir Mamman, ministan ilimi; Wale Edun; Ministan kudi da Abubakar Kyari, ministan noma, da Mustapha Shehuri da sauransu ne suka halarci tattaunawar.
Iftila’i: Gobara ta Hallaka Wani Yaro Dan Shekara 4 a Kano
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito mawuyacin halin da al’ummar Nigeria suke ciki sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar, wanda ya janyo tsadar rayuwa.
Hakan ne dai ta haddasa Zanga-Zangar lumana a jihar Neja, inda daruruwan mutane suka fito domin nuna damuwarsu kan halin da suke ciki na tsadar kayan Abinchi.