Tsadar Abinchi: Abubuwa 3 da Gwamnan Kano Ya Fadawa Yan Kasuwa Yayin Ganawar sa Da Su

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

1. Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yace zai nemi shugaban kasa Bola Tinubu ya sa baki domin magance matsalar yunwa dake addabar al’ummar jihar.

“Ni da kaina zan je na roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani ya duba halin yunwa da ake fama da shi a jihar Kano, domin ceto mutanenmu daga yunwar,” in ji Yusuf.

“Mun san cewa sauran sassan kasar nan suna fuskantar irin wannan abu, amma za mu je da maganar jihar Kano ne, saboda anan jama’ar mu suke ,” inji shi.

Kotu ta sanya ranar saurarar karar da aka shigar don kalubalantar hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar

Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan kasuwar jihar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano a ranar Litinin.

Ya ce lamarin ya yi kamari, don haka dole ne Gwamnatin Tarayya ta sa baki don fitar da jama’a daga halin da ake ciki.

An kira taron ne a karo na biyu, domin tattauna halin da ake ciki a harkokin kasuwanci, musamman a kan tsadar kayayyaki, da nufin samar da mafita ga matsalar da al’umma suke ciki.

Rundunar Yan sandan Kano Ta Kama Wani Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane

2. Gwamnan ya koka da yadda ake fama da matsalar yunwa a jihar, inda jama’a musamman talakawa ke fama da matsalar cin abinci sau uku a rana.

A cewar sa, lamarin ya kara tabarbare ne sakamakon tashin farashin kayan masarufi musamman shinkafa da masara da wake da gero wanda ya ce hakan ya sa jama’a ba sa iya siyan kayayyakin.

3. Don haka ya bukaci ‘yan kasuwa da suka hada da masu sana’o’in hannu da masu sayar da kayayyakin masarufi su sayar wa jama’a a farashi mai rahusa domin rage musu radadi.

“Ina kira gare ku da ku fito da kayan abinci da sauran kayan masarufi daga cikin ma’ajiyar ku ku sayar wa jama’a a farashi mai rahusa domin a samu saukin halin da suke ciki,” inji Yusuf.

 

Prime Time News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...