Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani Isa Lawal da ya shahara wajen garkuwa da mutane da tare shanu 55 a karamar hukumar Karaye da ke jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Malam Hussaini Gumel ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane ce ta kama shahararren mai garkuwa da mutanen.
INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu
“A ranar 4 ga watan Fabrairu da misalin karfe 17:40 ne aka kama Isa Lawal wani dan bindiga mai garkuwa da mutane a kauyen Kaya dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a karamar hukumar Karaye dauke da shanu 55, da tumaki 6.”
CP ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa sun gudu ne daga sansanin ‘yan bindigar Maidaro ta karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna bayan sun yi artabu da ‘yan bindigar da ke karkashin jagorancin Boderi Isiya na suke zaune a wuri gudana .
“Wanda ake zargin ya bayyana sunan shugaban kungiyar su mai suna Bashir Snu na karamar hukumar Malfashi ta jihar Katsina, wanda aka kashe a fadan da wani kwamanda Muazu Snu da suka gudu da bindiga kirar AK47 guda uku da kuma shanu da dama.”
CP Mohammad Hussein Gumel ya bayyana cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa suna shirin zama a dajin Gwarzo da kuma na karamar hukumar Karaye.
Ya kuma bayyana cewa ya shiga hannu tare da wasu ‘yan sansanoni da dama da suka kware wajen yin garkuwa da mutane da satar shanu a jahohin Kaduna, Katsina da Zamfara tare da shugabansu Muazu Mai Bokolo na karamar hukumar Malufashi ta jihar Katsina wanda yanzu haka ya tsere da bindiga kirar AK47 guda uku.
Ya kuma yi bayanin cewa wasu mutane hudu da ake zargi, Yalo, Bala, Ibrahim da Sunusi guda daya suma sun tsere.
“Tun daga lokacin da muke gudanar da bincike mai tsanani kuma mun kama wadanda ake zargin tare da kwato makamai a wajen su.”
Gumel ya ba da tabbacin hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da samar da isasshen tsaro ga al’ummar jihar kano da kasa baki daya .