Ofishin shugaban Najeriya ya tayar da kura da iƙirarin da ya yi na cewa kasar ta fi ƙarancin tsadar rayuwa a nahiyar Afirka.
Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya fadi hakan a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake yin watsi da sukar da Atiku Abubakar ya yi cewa manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu na ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.
Mista Onanuga ya bayyana wani nazari da wani kamfani intanet Numbeo ya yi kan matsayin Najeriya a tsarin tsadar rayuwa.
Rundunar Yan sandan Kano Ta Kama Wani Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane
Ya ce cibiyar tattara bayana ta Numbeo ta ce Najeriya ce ke da maki mafi girma wajen samun araha.
Amma hakan ba ya cikin dukkan ƙasashe 54 na Afirka, domin kasashe 23 ne kawai a nahiyar aka gudanar da binciken a kansu.
Matsayin Najeriyar zai iya yi wa ‘yan kasar dadi kadan – wadanda ke fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci da kayan masarufi, da asarar tallafin man fetur, da kuma karancin kudi.