Yadda Yan Sanda Suka Kama Shugabar Mata Masu Gurasa Da Suka Yi Zanga-Zanga A Kano Jami

Date:

 

 

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama Fatima Auwal, shugabar matan da jagoranci masu gurasar da suka gudanar da zanga-zangar lumana , a Kano a makon daga gabata.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jakara ce ta kama ta a ranar Asabar.

Jaridar KADAURA24 ta ruwaito cewa zanga-zangar da masu yin Gurasar suka yi a Kano ranar Alhamis sun yi ne kan tsadar farashin fulawa .

INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu

Rahotanni sun nuna cewa an kama Fatima Auwal ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan sanda suka samu daga wasu mata biyu da wani mutum da suka ce ita ba ‘yar kungiyarsu ba ce, don haka ba ta da hurumin yin amfani da sunan su har ta jagoranci zanga-zanga .

Ko da yake majiyar kadaura24 ta Solacebase ta tabbatar da cewa daga baya an sake ta a matsayin beli da yamma bayan wasu sun shiga maganar, ta kuma bukaci ta dawo ofishin ‘yan sanda a yau Lahadi.

Da take zantawa da SOLACEBASE kan lamarin, Fatima Auwal, ta ce ta yi mamakin tambayar da ‘yan sanda suka yi mata kan zanga-zangar lumana da ta yi da nufin fadawa gwamnati mawuyacin hali da suka shiga sakamakon tashin farashin fulawa.

” ‘Yan sandan sun ce wasu mata da wani mutum ne suka yi korafin cewa mun yi amfani da sunan kungiyarsu yayin zanga-zangar wanda hakan ba gaskiya ba ne”. A cewar Fatima Auwal

Yanzu-yanzu INEC ta Bayyana Dalilan ta na Dkatar da Zaɓen Kunchin da tsanyawa

‘’Mutanen da suka shigar da korafin su ne masu sayar da gurasa ne, alhali mu kuma mu ne masu hada ta gurasar. Don haka ya ba ni mamaki cewa sana’ar da mutane da yawa suka san mu akai za’a ce munyi sojan gona akan ta.’’

‘’Eh ‘yan sanda sun nemi da in dawo ofishina yau bayan an sake ni a matsayin beli jiya da daddare.

Da yake mayar da martani kan wannan al’amari, Shugaban kungiyar Jakara Junction Gurasa Bakers, Multi-Purpose Cooperative Society, Hadiyyatulahi Hamisu ya tabbatar da cewa su ne suka shigar da korafin a wajen ‘yan sanda kan amfani da sunan kungiyarsu da masu zanga-zangar suka yi.

Ko da yake Hamisu ya ce shugabar zanga-zangar, Fatima Auwal ita ma mai yin burodin Gurasa ce kuma ita ce shugabar karamar kungiyar masu gurasa.

”Shi ya sa muka kai karar ‘yan sanda.”

”Abin da muke nema a gare ta shi ne ta koma kafafen yada labarai ta janye maganarta.”

Hadiyyatulahi wanda shi ma ya tabbatar da hauhawar farashin na fulawa, ya ce kalubalen tattalin arziki ne na yau da kullum da ake fuskanta a ko ina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...