Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana sanya idanu tare da gudanar da bincike kan wasu rahotonnin samun hatsaniya a zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwa wasu jihohin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta samu rahoton cewa wasu ɓata gari sun sace kayayyakin zaɓe a wasu wurare a jihohin Kano da Akwa Ibom da kuma Enugu.
Sakon Rundunar Yan sandan Kano ga Al’umma Game da Zaɓen da Za’a Yi Gobe Asabar
Sanarwar INEC ɗin ta ce an samu tsaiko a rumfuna 10 na ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa a jihar Kano, inda ake gudanar da zaɓen ‘yan majalisun dokokin jihar.