Siyasar Kano: Tinubu Ya Baiwa Kwankwaso da Ganduje Umarni

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya fara yunkurin sasanta jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso da kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, a kokarinsa na tunkarar shekarar zabe ta 2027 domin sake komawa shugabancin Nigeria a karo na biyu.

Wasu majiyoyi da dama sun tabbatar wa da Jarida Daily Trust a ranar Litinin da ta gabata cewa shugaban ya bayyana aniyarsa ga shugabannin biyu a lokuta daban-daban, inda kuma ya ba su wa’adin wani lokaci domin su sanar da masu ruwa da tsakin da suke jagoranta manufarsa, sannan su dawo nan gaba kadan don yin sulhun.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da wasu zababbun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga jihar Kano, sannan kuma ya gana da Kwankwaso a ranar Lahadin da ta gabata, duk a kokarinsa na jagoranta sulhunta tsaffin gwamnonin jihar Kanon guda biyu, Inda ake sa ran zasu je da mutane biyu kowannensu.

Muna daukar matakan dakatar da dauke wasu hukumomin gwamnatin tarayya zuwa Lagos – Sanatocin Arewa

Wasu majiyoyi na kusa da Ganduje sun tabbatar da cewa shugaban ya bukaci shugaban na APC da ya gana da masu ruwa da tsaki na APC a Kano a ranar Alhamis, sannan ya fara aikin tabbatar da hadin kai a tsakaninsu.

Rahotanni sun nuna cewa, yunkurin da shugaban kasa ya yi na tabbatar da hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano na da nasaba da irin kalaman batanci da yan jam’iyyar reshen jihar suke yi masa, saboda rawar da suke tunanin Tinubu ya taka a hukuncin da kotun koli ta yanke wanda bai baiwa dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 28 ga Maris, 2023, Dakta Yusuf Nasiru Gawuna nasaba .

Sabanin abin da ke faruwa na cewa shugaban kasa ya umarci shugaban (Ganduje) na kasa da ya sasanta da Kwankwaso, shugaban bai yi maganar Kwankwaso ba yayin taron masu ruwa da tsaki a fadar shugaban kasa, a makon jiya. A yayin ganawar, shugaban ya yaba da dabarun samar da sulhu da Ganduje yayi amfani da su a Ondo da Edo, kuma ya ce yana son ya yi irin wannan dabarun da Kano”, kamar yadda daya daga cikin majiyoyin da suka shiga taron ya shaida wa majiyar kadaura24.

Abubuwa 5 da Tinubu ya fadawa Ganduje, Gawuna da shugabannin APC na Kano

Majiyar ta kara da cewa a wata ganawar sirri da Tinubu da Ganduje suka yi, shugaban kasar ya sanar da shugaban jam’iyyar APC aniyarsa ta shigo da Kwankwaso cikin APC, sannan ya bukaci shugaban da ya fito da dabarun cimma wannan manufa. A matsayin matakin farko na cimma wannan buri, shugaban ya roki Ganduje da ya kira taro a Kano, domin sanar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a wajen taron da aka yi a Abuja, sun nuna ra’ayinsu game da abin da shugaban kasar ya ba da shawara, amma kuma konnensu ya kasa fitowa karara ya nuna adawarsa da shawarar Tinubun.

Ganawar Tinubu da Kwankwaso

Daily Trust ta gano cewa kwanaki uku bayan ganawarsa da Ganduje da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar Kano, shi ma shugaba Tinubu ya gana da Kwankwaso.

Taron wanda aka gudanar a fadar Villa a ranar Lahadin da ta gabata. Duk da dai ba a san takamaimai abin da ganawar ta kunsa ba, amma majiyoyi na kusa da jagoran jam’iyyar NNPP sun bayyana cewa an sanar da Kwankwaso yunkurin sulhun.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa majiyar kadaura24 cewa shugaban ya bayyana matakin da ya dauka na kiran wani taro inda za a warware sabanin da ke tsakanin Ganduje da Kwankwaso.

“Shugaban kasa ya ce masa (Kwankwaso) ya je ya gana da masu ruwa da tsaki na tsaginsa kamar yadda ya bukaci Ganduje ya yi. Daga nan sai shugaban ya ce su biyun su koma wurinsa da mutane biyu kowannensu domin yin wani taron da za a yanke hukunci na karshe kan batun sulhun,” inji daya daga cikin majiyar mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...