Gwamnan jihar Filato, Calbe Mutfwang ya ayyana dokar hana fita – daga safe zuwa dare a karamar hukumar Mangu.
Dokar za ta soma aiki nan take.
Matakin na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai da harkokin al’umma na jihar, Gyang Bere ya sanyawa hannu.
Siyasar Kano: Tinubu Ya Baiwa Kwankwaso da Ganduje Umarni
Ya ce an dauki matakin ne saboda tabarbarewar harkokin tsaro a yankin.
Sanarwar ta kara da cewa “gwamna Mutfwang ya dauki matakin bayan tuntuba da ya yiwa hukumomin tsaro.”
Muna daukar matakan dakatar da dauke wasu hukumomin gwamnatin tarayya zuwa Lagos – Sanatocin Arewa
Matsalar tsaro na ci gaba da karuwa a jihar ta Filato. Ko a baya-bayan nan an kai wasu jerin hare-hare da suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 da jikkatar wasu da dama. An kuma kona wasu gidaje.