Cikakken Bayani da Dalilin Yadda aka Gurfanar da Danbilki Kwamanda a Kotu

Date:

An kama babban ɗan’adawar nan na Kano Danbilki Kwamanda tare da tasa keyarsa zuwa gidan yari.

Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda bisa zargin yin wasu maganganu da ake zargin za su iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano.

Siyasar Kano: Tinubu Ya Baiwa Kwankwaso da Ganduje Umarni

Hukumar DSS ce ta fara gayyatarsa tare da miƙa ga shi ƴan sanda, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar wa BBC.

“Ana zarginsa da yin wasu kalamai na tunzura jama’a kan batun masarautu a jihar Kano,” in ji shi.

Sai dai ya musanta zargin da ake ma sa a kotun.

Zauren Dattawan Kano: Dattawan Jihar Sun Fara Mayarwa Farfesa Tijjani Naniya Martani

Ya yi kalaman ne a wani gidan rediyo a Kano, bayan kalaman jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun makomar masarautu a jihar ta Kano.

A cikin kalamansa da suka janyo kama shi, Danbilki ya ce ba za su yarda da cire sarakunan ba.

Kotu ta bayar da umarnin tafiya da shi zuwa gidan gyaran hali na Goron Dutse a Kano.

Sai a ranar 29 ga watan Janairu kotu za ta saurari buƙatar belinsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam...